Putin: Rasha na da sabbin makamai masu linzami | Labarai | DW | 01.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Putin: Rasha na da sabbin makamai masu linzami

Shugaban Rasha Vladimir Putin yace Rasha ta mallaki sabbin makamai masu linzami yayin da a waje guda ya ci alwashin rage talauci a tsakanin al'umma a kasar.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace kasarsa ta kera sabbin makamai masu linzami da za su iya kai hari ko ina a duniya da kuma wani makamin na karkashin ruwa da aka inganta wanda zai yi wuya abokan gaba su iya cin masa.

Putin ya kuma ce Rasha ta yi gwajin wani sabon makami mai linzami mai cin dogon zango da ta yiwa lakabi da Sarmat wanda ya zarta wadanda kasar ta mallaka a baya.

Da yake jawabi ga jami'an gwamnati da yan majalisun dokoki Vladimir Putin ya zargi Amirka da saba alkawarin daidaiton makamai a saboda haka yace akwai bukatar Rasha ta samar da ingantacciyar fasaha domin share fagen nasarori da wanzuwar cigaba.