Puigdemont ya mika kansa ga hukumomi | Labarai | DW | 05.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Puigdemont ya mika kansa ga hukumomi

Jagoran 'yan awaren kafa yankin Kataloniya Carles Puigdemont tare da wasu tsoffin ministoci, sun mika kansu a gaban shari'a. Hukumomin kasar Beljium sun ce ba wanda ya tilasta wa mutanen zuwa ofishin 'yan sanda.

A yanzu dai babban mai gabatar da kara na kasar Beljium ya ce za su ci gaba da yin nazari kan takardar somame da Sapaniya ta aikewa kasar. Nan da lokaci kadan alkalin zai yanke hukunci kan jagoran 'yan awaren na Kataloniya da sauran mutanen hudu, domin sanin ko za a ci gaba da tsare su ko za a ba da belin su a kan wasu ka'idoji. Spain:Sammaci ga shugaban yankin Cataloniya

A tun ranar Jumma'a ne dai Carles Puigdemont ya tsere daga kasar Spaniya zuwa neman mafaka a kasar Belgium, bayan da mahukuntan Spaniya suka haramta zaben neman kafa yankin Kataloniya.An fara shari'ar maharan Spain

 

DW.COM