1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Premier Wen na Sin a Congo

Zainab A MohammedJune 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6X

A cigaba da rangadin aiki a wasu kasashen Afrika guda 7,Premiern Sin Wen Jiabao ya isa janhuriyar congo da yammacin yau,inda shugaba Denis Sassaou Nguesso ya marabceshi a birnin Brazzaville.Anasaran shugabannin biyu zasuyi ganawa ta musamman a fadar shugaban kasar ayau,wanda zai inganta dangantaka tsakanin kasashen nasu.Sanarwar majiyar jamian Sin din dai,na nuni dacewa bangarorin biyu zasu rattaba hannu a yarjeniyoyi,kana a gobe talata Premier Wen zai zai gana da alummar yan kasar sin 500,dake gudanar da harkokin kasuwanci a congo,kana zai ziyarci daya daga cikin asibitoci biyu da gwamnatin Beijing ta gina,wanda ke dauke da likitocin sin din.

Bugu da kari Shugaban gwamnatin na Sin zai gana da daliban manyan makarantun kasar dake nazarin ilimin harshen sinanci a Congon,kafin ya wuce kasar Angola.Harkokin ciniki tsakanin kasashen biyu dai yakai kwatankwacin dalan Amurka Billion 2.05a shekarata 2005,inda Sin take shigowa da maid a katako,kana tana fitar da kayayyakin da aka kamala sakarsu da kayan gini.