Poland za ta rufe wasu manyan gine-gine a kasar. | Labarai | DW | 30.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Poland za ta rufe wasu manyan gine-gine a kasar.

Gwamnatin kasar Poland, ta ba da umarnin rufe wasu manyan gine-gine a duk fadin kasar, a cikinsu har da manyan kantuna, wadanda ake zaton tsarin gina su bai dace da yanayin sanyi na yankin da kasar ke ciki ba, abin da ke janyo rushewarsu a lokuta kamar na yanzu inda ake bala’in sanyi. A hadarin da ya auku a garin Katowice a karshen makon nan, inda rufin wani zauren nunin kayayyakin baje koli ya burmo kan jama’a, mutane 67 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu dari 50 kuma suka ji rauni. Jami’an kiwon lafiya a garin dai sun ce yawan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin zai iya tashi, saboda mummunan halin da wasu daga cikin wadanda suka ji raunin ke ciki. Har ila yau dai ba a gano wasu mutane 15 da ke karkashin tarkacen ginin ba tukuna, amma jami’an ceto sun ce sun fid da tsammanin samun wani daga cikinsu da rai.