Jam'iyyar PJD ta sha kaye a zaben Maroko
September 9, 2021Talla
Gungun jam'iyyun 'yan adawa ne dai suka kifar da jam'iyyar a yayin zaben kasar da aka yi a jiya, bayan da suka lashe kujeru mafi rinjaye na 'yan majalisun dokokin Marokon kasar 395, a yayin da jam'iyyar PJD ta samu kujeru 12 kawai, lamarin da ya takaita burinta na karin wa'adi na uku a kan madafan iko.
A yanzu Sarki Mohammed na VI ne ke da hurumin nada daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyun da suka yi rinjaye a matsayin sabon shugaban gwamnati, kana kuma ya gayyaci jam'iyyun da su gabatar da wani sabobon tsari na raya kasa da zai dace da sabbin manufofin sarkin na sauye-sauye a kasar.