Pistorius, zai fito daga gidan yari | Labarai | DW | 31.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pistorius, zai fito daga gidan yari

Tsohon zakara a gasar tseren nakasassu na Afirka ta Kudu, Oscar Pistorius, wanda yanzu haka ake tsare da shi a gidan kurku saboda laifin kisan budurwarsa, za a iya sakinsa nan gaba dan.

Dokar Afirka ta Kudu ta tanadi cewa wanda aka samu da laifin kisan kai, zai iya amfana da sakin da wuri da zarar rabin hukuncin da aka yanke masa ya cikka. Dan wasan  mai shekaru 36, wanda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 da watanni 5 na zaman  gidan yari, a shekara ta 2013  bayan kashe masoyiyarsa ya zama gwarzon dan wasa, a gudun panpalaki a gasar Olympics ta nakasasu a shekarar ta 2012.