Pirsinonin Yan taliban 2 sun sauka a Seoul | Labarai | DW | 17.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pirsinonin Yan taliban 2 sun sauka a Seoul

Bayan kussan wata daya na uƙuba da azaba, Korewan nan 2 da yan taliban su ka saki ranar litinin da ta wuce sun sauka yau abirnin Seoul.

A yayin da ta ke jawabi tare da yan jarida, ɗaya da cikin tsafin pirsinonin wato Kim Kyung_Ja, ta nemi gafara ga jama´a a game da fadi ka tashin da su ka yi ta yi na samun beli.

Sannan ta yi fatan dakarunTaliban su yi belin sauran pirsinonin da ke cikin hannun su.

Yau wata kena da ya gabata yan taliban su ka yi garkuwa da mutane 23 na Korea ta Kudu, wanda tunni su ka kashe 2 daga cikin su.

A jiya alhamis a ka kammalla wata tantanawa, tsakanin wakilianTaliban da na gwamnatin Korea ta Kudu, ba tare da cimma buri ba.

Ƙungiyar Taliban ta jadada bukatar ta, ta gwamnati ta saki wasu daga cikin dakarun ta, matakin da hukumomin Kabul su ka ƙi amicewa da shi.