Pilipin ta yi watsi da tallafin Kungiyar EU | Labarai | DW | 17.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pilipin ta yi watsi da tallafin Kungiyar EU

A cewar Jakada Franz Jessen da ke zama mai kalubalantar gwamnatin Shugaba Rodrigo Duterte daukar matakin yanke wannan tallafi daga EU na nufin al'ummar Musulmi su rasa miliyan 250 na Euro.

Gwamnatin Pilipin ta fadawa Kungiyar Tarayyar Turai cewa ba za ta sake karbar tallafi daga kungiyar ba bayan karbar tallafi daga kasar China, matakin da ke nufin kokari na sanya al'ummar da ke cikin garari na neman agaji a Kudancin kasar cikin sabon garari a cewar jakada daga kungiyar ta EU.

A cewar Jakada Franz Jessen da ke zama mai kalubalantar yaki da miyagun kwayoyi da gwamnatin Shugaba Rodrigo Duterte ke yi daukar matakin yanke wannan tallafi daga EU na nufin al'ummar Musulmi da ke cin moriyar shirin Kungiyar EU za su rasa miliyan 250 na Euro.

Kungiyar EU dai na bada tallafi ga mahukuntan na Manila a kokarinsu na kawo karshen tawaye na Musulmi tsawon shekaru 50 abin da ya yi sanadi na rayukan sama da mutane 120,000 da sanya kimanin miliyan daya rasa muhallansu.