Pilipin: Soji sun hallaka ′yan bindiga 50 | Labarai | DW | 30.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pilipin: Soji sun hallaka 'yan bindiga 50

Dakarun Pilipin sun hallaka tsageru masu dauke da makamai fiye da 50 masu kaifin kishin addinin Islama lokacin artabu a yankin kudancin kasar.

Rahotanni daga kasar Pilipin sun ce dakarun kasar sun hallaka kimanin tsageru masu dauke da makamai 54 masu kaifin kishin addinin Islama. Mai magana da yawun sojojin kasar ya ce lamarin ya faru cikin yankin kudancin kasar.

Wannan rikici na tsawon shekaru 45 ya yi sanadiyar hallaka kimanin mutane 120,000 kuma yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekara ta 2014 ta na tangal-tangal. Tuni zababben shugaban kasar ta Pilipin Rodrigo Duterte ya yi alkawarin neman sulhu da tsagerun masu kaifin kishin addinin Islama, inda ya ce zai kara wa yankin karfin siyasa da tattalin arziki.