Petro Poroshenko ya lashe zaben Ukraine | Labarai | DW | 25.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Petro Poroshenko ya lashe zaben Ukraine

Attajirin nan na kasar Ukraine Petro Poroshenko ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a wannan Lahadin da kusan kashi 56 cikin 100.

Präsidentschaftswahlen in der Ukraine Poroschenko ARCHIV

Shugaban Ukraine mai jiran gado Petro Poroshenko

Jim kadan bayan bayyana wannan nasara da ya samu, Mr. Poroshenko ya ce gwamnatinsa za yi bakin kokarinta wajen ganin an gudanar da zabukan majalisar dokokin kasar a wannan shekara da muke ciki.

Shugaban na Ukraine mai jiran gado wanda kanwarsa ba ta jikuwa da gwamnatin Rasha ya ce zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ya tabbatar da 'yancin cin gashin kan kasarsa.

Mr. Poroshenko da ke dasawa da kasashen yamma ya kuma ce ba zai taba amincewa da hadewar da yankin nan na Kirimiya ya yi da kasar Rasha ba a watannin da suka gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe