Petraeus ya amsa laifin lalata | Labarai | DW | 10.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Petraeus ya amsa laifin lalata

Murabus da babban jami'in hukumar leken asirin Amirka, David Petraeus ya yi kwatsam ba zato ba tsammani, ya kawo karshen aikinsa cikin masu tafiyar da lamuran kasar.

Petraeus ya ajiye aiki ne saboda bincike da hukumar binciken manyan laifukan ta FBI, wadda ta gano cewa yana lalata da wata mace, wadda ake zargi ta samu bayanai na sirri daga wurinsa.

Shugaba Barack Obama ya amince da murabus din, amma wasu rahotanni na cewa da farko Obama ya nami Patraeus ya ci gaba da aikinsa, amma ya tsaya kai da fata cewa, abun da ya yi, ya saba yadda mutun kamarsa ya dace ya yi.

Haka ya kawo karshen aikin tsohon habsan sojan, Janar David Patraeus, wanda ya samu tsauraru hudu, kuma ya jagoranci dakarun kasar ta Amirka a kasashen Iraki da Afghanistan.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita:Halima Balaraba Abbas