Peter Mutharika ya yi rantsuwar kama aiki | Labarai | DW | 31.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Peter Mutharika ya yi rantsuwar kama aiki

A wani mataki na kawo ƙarshen taƙaddamar da ta biyo bayan zaɓen ƙasar Malawi a yanzu hukumar zaɓe ta ce ƙuri'un da aka ƙidaya, na nuna cewar Mutharika shi ya ci zaɓe kuma dole Joyce Banda ta miƙa mulki.

Hukumar zaɓen ƙasar Malawi, ta ayyana Peter Mutharika a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, inda ya lashe zaɓen da sama da kashi 36 cikin ɗari. Hukumar zaɓen ta sanar da Mutharika a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, bayan cece-kuce da aka samu, inda shugaba mai barin gado Joyce Banda, ta ƙi yarda da shan kaye. Wata babbar kutun ƙasar ta yi watsi da buƙatar shugabar mai barin gado na neman a soke zaɓen, bisa zargin yin maguɗi. Dama dai shugabar mai ci ta buƙaci a soke zaɓen, kana a gudanar da wani sabo bayan watanni uku, abin da kuma kotun ƙasar ta yi watsi da shi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdourahamane Hassane