1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Peter Greste na Aljazira ya koma gida

February 5, 2015

Ɗan jaridar da ya kwashe sama da shekara ɗaya cikin bakwai da aka yanke masa a Masar, ya kuma jaddada ci gaba da fafutikarsa a fagen na aikin jarida.

https://p.dw.com/p/1EVp0
Ankunft des australischen Journalisten Peter Greste in Brisbane
Peter Greste ma'aikacin Al-jazeeraHoto: picture-alliance/dpa/D. Hunt

Peter Greste ɗan jaridar ɗan asalin Ostareliya ya koma gida bayan an sako shi daga ƙasar Masar, Peter Greste ya kwashe sama da shekara guda a tsare bayan ɗaure shi da aka yi da nufin ya kwashe shekaru bakwai a gidan kaso saboda tuhume-tuhume da ake masa da suka haɗa da tallafa wa 'yan ta'adda.

Greste ya dai sauka a ƙasar ta Ostareliya a yau Alhamis inda ya yi jawabi ga manema labarai da ke dakon saukarsa a birnin Brisbane. Cikin jawabansa dai ya bayyana fatansa na ganin an sako 'yan uwansa da suka haɗa da Mohammed "

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdourahamane Hassane