PDP da APC sun fafata a zaben Ondo | Labarai | DW | 10.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

PDP da APC sun fafata a zaben Ondo

Hukumar zaben Najeriya na ci gaba tattara sakamakon zaben gwaman jihar Ondo inda sama da mutum miliyan daya suka kada kuri'unsu a zaben wanda takara ta fi zafi tsakanin jam'iyyar APC da PDP mai adawa.

Rahotanni na cewa ana cigaba a tattara sakamakon zaben a rumfunan da jama'a suka kada kuri'unsu a zaben wanda takara ta fi zafi tsakanin gwamna mai ci Rotimi Akeredolu na jam'iyyar APC da kuma Eyitaye Jagede na jam'iyyar PDP da ke adawa.

Duk da zarge-zargen juna da bangarorin siyasar kasar ke yi wa juna,kawo yanzu babu wasu rigingimun da aka hakikance sun wakana da suka fi karfin hukumar tsaro da ta jibge tarin 'yan sanda domin ganin an gudanar da zaben a cikin kwanyciyar hankali.

Zaben dai wani zakaran gwajin dafi ne ga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da ke fatan ta cigaba da jan zare a fagen siyasar kasar.