1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Kagame ya kama hanyar lashe zabe

Usman ShehuSeptember 17, 2013

Sakamakon farko na zaben kasar Ruwanda da aka fitar, ya nuna alamun jam'iyyar FPR da ke kan mulki, ita ce za ta yi nasara

https://p.dw.com/p/19jjh
Rwanda's President Paul Kagame casts his vote during a parliamentary election in the capital Kigali September 16, 2013. Rwandans voted in a parliamentary election on Monday that is widely expected to hand an easy win to the ruling coalition in a national assembly that may be asked to change the constitution to allow Kagame a third term.REUTERS/Jenny Clover (RWANDA - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Paul Kagame, a lokacin kada kuri'aHoto: Reuters

Zaben na bana dai an yi ittifakin yana gudana yadda ake bukata, batare da tashin hankali kamar yadda ake gani a mafi yawancin zabuka a nahiyar Afirka ba. Tunda sanyin safiya zabukan suka fara kankama sakamakon kaiwa kayan zaben da bayyanar jamai kan lokaci, hakan ya bai wa al'umma damar kada kuri'unsu cikin kankanin lokaci, inda wasun su ke komawa wuraren aikinsu ba tare da wani bata lokaci ba.

Bayyanar alkaluma da ke tabbatar da rinjaye ga bangaren jam'iyyar FPR mai mulki ta shugaba Paul Kagame, bai zo wa babbar jam'iyyar hamayya ta Green Party da wani mamaki ba, inda ta mayar da martani kan cewa ta san a rina, shi ya sa ta ki shiga zaben tunda farko. Dama dai a mafi yawan lokuta, masana a nahiyar Afirka na ganin ba sa fai jam'iyya mai mulki kan sha kasa a zabuka ba, ko wannan tunani yana iya tasiri kan zaben Ruwanda?.

Ra'ayin masu sa ido

A cewar masu sanya ido kan zaben irinsu Musa Silma, wannan fa dama ce ga shugabannin da ludayinsu ke kan dawo, babu inda aka taba ganin wani shugaba da zai so subucewar mulki daga hannun sa ba. Ko da yake tsarin mulkin kasar Ruwanda ya zo da komai cikin sauki, sabanin wasu kasashen da lashe zabe a matakin farko ke kasancewa babbar nasarar karshe ga jam'iyya mai mulki. A Ruwanda sauran guraben wakilci zai fito daga sauran jam'iyyu domin daidaito.

Martanin yan adawa

Tun bayan komawar kasar Ruwanda kan tafarkin zaman lafiya, tattalin arziki ya inganta, wanda ake ganin hakan ya taka muhimmiyar rawa, wajen cimma nasarar zama kan mulkin gwamnatin Kagame har na tsawon shekaru 20. Ko da yake ga jam'iyyar Democratic Green Party, shiga wannan zabe a gare ta bata lokaci ne kawai. Sai dai ga matasa irinsu John Muga demukradiyyar Ruwanda jaririya ce, da ke bai wa kowa damar fadin ra'ayinsa dai-dai bukatar kai.

Yancin mata da naƙasassu

Kimanin guraben wakilci 53 ne daga cikin 80 al'ummar kasar suka zaba, yayinda a rana ta biyu da ta uku mata da matasa da nakasassu za su kasafta ragowar guraben wakilci 27 da su ka yi saura a tsakanin su. A cewar Musa Silma akwai gamsuwa game da yadda zaben ya gudana cikin lumana, zabe ne da ya banbanta da yadda ake gani a wasu wurare, saboda mun lura da gudummuwar kashin kai da ma'aikatan zaben ke bayarwa.

A ranar Larabar nan ake shiga rana ta 3 kuma rana ta karshe da zaben zai kammala, kamar yadda aka tsara, illa iyaka a jira sakamakon karshe daga hukumomi.

Mawallafi: Garzali Yakubu

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani