1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Paul Kagame na Ruwanda ya lashe zaben shugaban kasa

Binta Aliyu Zurmi
July 16, 2024

Sakamakon farko na babban zaben kasar Ruwanda na nuni da cewar Shugaba Paul Kagame ne ya sami gagarumar nasara, inda ya lashe zaben da kaso 99.15% na kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/4iLzZ
Präsidentschaftswahlen in Ruanda
Hoto: Brian Inganga/AP Photo/picture alliance

Zaben da ya gudana tsakanin Shugaba Kagame da wasu 'yan tara biyu, ya sami mafi akasarin kuri'un yayin da abokan takarar tasa Frank Habineza na jam'iyyar DGPR da kuma dan takara mai zaman kansa Philippe Mpayimana sun sami kasa da kashi daya na kuri'un zaben.

Shugaba Kagame da ke kan madafun iko tun bayan kawo karshen kisan kiyashin kasar a shekarar 1994, wannan nasara ta share masa hanyar darewa a wani wa'adi na 4 na tsawon shekaru biyar. Alkaluma sun nunar da cewar kuri'un da ya samu a wannan karon sun zarta na zaben shekarar 2017.

Hukumar zabe kasar Ruwanda ta ce za a fitar da cikaken sakamakon zaben a ranar 27 na wannan watan da muke ciki.

Kagame ya kasance shugaban Ruwanda da ya fi dadewa a kan madafun iko kuma yana daga cikin shugabannin Afirka da suka sauya kundun tsarin mulkin don samun damar ci gaba da shugabanci.