1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Biya ya zarce kan mulkin Kamaru

October 22, 2018

Shugaba Paul Biya da ke zama shugaban kasa mafi yawan shekaru a Afirka, ya sake lashe zaben shugaban kasa da aka yi a ranar bakwai ga watan Oktoba.

https://p.dw.com/p/36xTb
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Shugaban dan shekaru 86 zai ci gaba da zama a karagar mulki har sai shekarar 2025 lokacin da zai kai shekaru 93 da haihuwa.

Shugaba Biya dai shi ya kwashe sama da kashi 70 cikin dari na kuri'u kana Maurice Kamto na jam'iyyar CRM shi ya zamo na biyu, sai kuma Cabral Libii na jam'iyyar Universe ya zamo na uku.

Gabanin bayyana sakamakon, sai da aka baza jami'an tsaro a manyan birane tare da haramta duk wani gangami da 'yan adawa ka iya yi a kasar.

Bayanai sun ce gabanin sanar da sakamakon, an ga wasu dakarun gwamnati a gidajen manyan 'yan takaran adawa, wadanda suka yi kiran 'yan Kamaru da su kare 'yancinsu, muddin sakamakon da aka bayyana ya ci karo da abin da suka zaba.

A share guda kuwa wasu bayanan na cewa an ji amon harbe-harbe a yankin kasar na renon Ingila da wasu ke neman ballewa.