1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru da rinjaye

October 18, 2011

Sakamakon wucin gadi na zaɓen shugaban ƙasar Kamaru da aka bayyana ya nunar da cewa Paul Biya ya zo na ɗaya da kashi 77 % na ƙuri'un da aka kaɗa, gaban madugun 'yan adawa John Fru Ndi na SDF wanda ya zo na biyu da 10%.

https://p.dw.com/p/12utH
Paul Biya mai shekaru 78 zai ci gaba da mulkin KamaruHoto: dapd

Wani jami'in kamaru da ya halarci zaman tantace ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa ya nunar da cewa Paul Biya mai barin gadi ya samu gagarumin rinjaye kamar yadda aka yi hasashe tun da farko. Sakamakon wucin gadi na zaɓen tara ga watan oktoba ya nunar da cewa shugaba Paul Biya wanda ya shafe shekaru 29 akan karagar mulki ya lashe kashi 77 % na ƙuri'n da aka kaɗa. Yayin da madugun 'yan adawa na kamaru wato John Fru Ndi na jam'iyar SDF da ya zo na biyu ya tashi da kashi 10% na ƙuri'un. Ita dai kotun ƙoli da ke maye gurbin kotun tsarin mulki na da wa'adin 24 na wannan wata na oktoba domin bayyana cikakken sakamakon zaɓen da ke zama na uku tun bayan da kamaru ta rungumin tsarin jam'iyu da dama.

Tuni dai jam'iyun adawa suka yi watsi da sakamkon zaɓen saboda a cewarsu ya na cike da kura-kurai. Kana sun bukaci kotun ƙolin kamaru ta soke zaɓen, tare da rusa hukumar zaɓe mai zaman kanta da ake yi wa laƙabi da ELECAM saboda waɗanda suka danganta da 'yan koran gwamnati ne suke shugabantarta. 'yan takara da suka haɗa da John Fru Ndi na SDF, da Adamu Ndam Njoya na UDC da kuma Kah Wala ta CPP sun yi kira ga magoya bayansu da suka gudanar da zanga-zanga domin nuna ɓacin ransa game da maguɗin da aka tafka a zaɓen na shaugaban ƙasa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar