Park Geun Hye ta sami nasara a zaɓen Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 19.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Park Geun Hye ta sami nasara a zaɓen Koriya ta Kudu

Yar takarar jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya yar kimanin shekaru 60 za ta kasance macce ta farko da za ta riƙe matsayin shugaban ƙasa a Koriya ta Kudu

A cikin kishi sama da tamanin na ƙuri'un da aka ƙidaya ta samu kishi 51 da yan ka a gaban abokin hamayarta Moon Jae In wanda tuni ya amince ya sha kaye

Park yar tsohon shugaban gwamnatin mulkin kama karya Park Chunk Hee wanda ya zo akan karagar mulki a shekara ta 1961 kafin a kashe shi a shekara ta 1979.Zata kasance mace ta farko da za ta riƙe matsayin shugaban ƙasar da za ta fara wa'adin mulki na shekaru biyar a cikin watan feberu na tafe.

sama da mutane miliyion 40 ne dai suka kaɗa ƙuri'u a zaɓen shugaban kasar da aka ce jamaa da dama sun fito.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman