Paris: Wani mutum ya kaiwa 'yan sanda hari | Labarai | DW | 07.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paris: Wani mutum ya kaiwa 'yan sanda hari

'Yan sandan Faransa sun harbe wani mutum har lahira bayan da ya tinkari wani caji ofis dazu sanye da riga ta kunar bakin wake da kuma wuka a hannunsa.

Wani mutum da ya shaida faruwar lamarin wanda ya auku a birnin Paris ya ce mutumin ya yi ta kabbara da babbar murya lokacin da ya doshi ofishin 'yan sandan, sai dai bayan da aka hallaka shi an gano cewar rigar kunar bakin waken ta jabu ce.

Tuni dai aka jibge jami'an tsaro da kuma kwararru da ke kwance abubuwa masu fashewa a inda abin ya faru. Yanzu haka dai kwararrun na can suna cigaba da gudanar da bincike. Ya zuwa yanzu ba a kai ga bayyana sunan wannan mutumi ko ma kasar da ya fito ba.

Lamarin dai na zuwa ne jim kadan bayan kammala jawabin Shugaba Francois Hollande, shekara guda bayan da aka kai hari kan gidan jaridar nan ta Charlie Hebdo da ke zane-zanen barkwanci.