Paris club tace zata yafewa saliyo bashi | Labarai | DW | 24.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paris club tace zata yafewa saliyo bashi

Kungiyar Paris club ta sanarda da cewa zata yafewa kasar Saliyo bashin dala miliyan 218 da take binta a ci gaba da kokarin da kasashen duniya sukeyi na taimaka kasar farfado da tattalin arzikinta.

Shekaru biyar bayan yakin basasa na kasar ta Saliyo kasashen duniya sun fara maida hankalin kann kasar musamman saboda kokari da takeyi na rage cin hanci da rashawa da yakar talauci tsakanin alummominta.

Kasar ta sasliyo ta kaddamar da shiryuka na karfafa tatalin arzikinta .

A watan disamba na bara bankin duniya da IMF sunce Saliyo ta cancai a yafe mata bashin dala biliyan 1.6 da ake binta karkashin shirinsa na yafe basuka.