Paparoma ya yi kira ga matasan kasar Kuba da su hada kai | Labarai | DW | 21.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya yi kira ga matasan kasar Kuba da su hada kai

A ganawar da ya yi da daruruwan matasa a birnin Havana, Shugaban 'yan Katholika a duniya ya ce ka da matasan su bari a sanya musu tarnaki.

A ci gaba da ziyarar da yake kai wa kasar Kuba Paparoma Francis ya yi kira ga matasan kasar da kar su bari a yaudaresu da wasu akidoji da za su zamesu wani tarnaki kan muradunsu na neman cigaba. Paparoma ya yi wannan kira ne lokacin ganawarsa da wasu daruruwan matasa a Havana babban birnin kasar ta Kuba. Da farko ya gana tsawon mintuna 30 da jagoran juyin juya hali kuma tsohon shugaban Kuba Fidel Castro a gidansa, inda suka tattauna kan batutuwan da suka hada da kare muhalli da dai sauransu. Daga bisani sun yi musayar littattafai tsakaninsu. A kuma halin da ake ciki Paparoma Francis ya isa Holguin da ke zama birni na uku mafi girma da ke a gabashin kasar, inda tuni dubun dubatan mutane suka yi cincirindo a dandalin da Paparoman zai jagorancin sujjada ta wannan rana.