Paparoma ya nemi gafarar musulmin Bama | Labarai | DW | 01.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya nemi gafarar musulmin Bama

A wannan Juma'ar, Shugaban darikar Katolika a duniya Paparoma Francis, ya nemi gafara daga wajen musulmin Bama dake zaman mafaka a kasar Bangaladash.

Bangladesch Dhaka - Papst Franziskus besucht Rohingya Flüchtlinge (Reuters/M. Rossi)

Paparoma Francis a ziyarar da ya kai Bangaladash

Wannan ne karon farko da Paparoma Francis ya kira sunansu musulmin na Bama, wato 'yan Rohingya a ziyarar da yake yi a kasashen Myanmar da Bangaladash. Shugaban na mabiya akidar ta Katolika, ya ce ya roki gafarar ce a madadin wadanda suka wulakanta su da ma juya masu baya da wasu manyan kasashe suka yi yayin da suke cikin matsala.

Shi dai Paparoma ya ki ambaton sunan musulmin na Bama ne lokacin da yake a kasar Myanmar, inda Cocin Katolika dake kasar ta bukaci ya girmama ra'ayoyin al'umar kasar da ke da rinjaye. Ita dai al'umar ta Rohingya, na matsayin tsiraru ne a Myanmar.