1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya koka kan rikicin Al-Aqsa

July 23, 2017

Paparoma Francis ya bayyana damuwa kan rikicin baya-bayan nan tsakanin Isra'ila da Falasdiwa kan masallacin Al-Aqsa, lamarin da ya ce a hanzarta zaman neman fahimta tsakanin juna.

https://p.dw.com/p/2h1aS
Vatikan - Papst Franziskus bei seiner Wöchentliche Ansprache
Hoto: Reuters/T. Gentile

A jawabin da ya yi wa masu ziyarar ibada a dandalin St. Peters a wannan Lahadin, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya yi fatan bangarorin biyu za su yi gaggawar fito da bukatar samun fahimtar juna. Arangama tsakanin Falasdinawa da jami'an 'yan sandan Isra'ila a ranar Juma'ar da ta gabata ta halaka mutane tara daga bangarorin biyu.

Masu aiko da rahotanni suka ce ana fargabar wutar rikicin ka iya karuwa. Jami'an Isra'ilan dai sun dauki tsaurara matakan tsaro ne tare da hana masallata sallah a masallacin na Al-Aqsa mai daraja ga musulmin duniya. Matakin da Isra'ilar ta gindaya shi ne sai wanda suka haura shekaru 0 da haihuwa da mata ne kadai za su sallah a masallacin maimakon kowa da kowa.