Paparoma Francis zai fara ziyara a Afirka | Labarai | DW | 31.01.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma Francis zai fara ziyara a Afirka

Shugaban darikar Katolika na duniya, Paparoma Francis ya fara ziyara a kasashen Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango da kuma Sudan ta Kudu domin neman a samar da zaman lafiya.

Wannan dai shi ne karo na biyar da Paparoma Francis zai kai ziyara nahiyar Afirka, kana karo na farko, tun daga shekarar 1985 da wani Paparoma ya kai ziyara Kwangon; wanda kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasar mabiya darikar Katolika ne. Tun a watan Julin bara ne dai aka tsara ziyarar kwanaki 6 ta Paparoman a Kwangon, sai dai saboda matsalar rashin lafiya aka dage ta a wancan lokacin.

Paparoma Francis dai ya koka kan yadda ake samun rikici tsakanin gwamnati da 'yan tawaye da kuma cin zarafin jama'a a Kwango tare da fatan kawo karshen rikici a Sudan ta Kudu.