paparoma Benedict na 16 ya yi kira ga Kirista da su guji son abin duniya | Labarai | DW | 26.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

paparoma Benedict na 16 ya yi kira ga Kirista da su guji son abin duniya

A ci-gaba da ziyarar da yake kaiwa kasar Poland Paparoma Benedict na 16 ya jagoranci wani bukin addu´o´i da ya gudana a wani filin Allah ta-alah a birnin Warsaw. A wannan wuri ne dai a shekara ta 1979 marigayi Paparoma John Paul na biyu ya yi kira ga ´yan Poland da su bijirewa mulkin kwaminisanci ba tare da wata fargaba ba. A lokacin bukin addu´ar na yau wanda ya gudana cikin yanayi na ruwan sama, Paparoma Benedict yayi kira ga mabiya darikar katholika su kimanin dubu 270 da suka hallara da su rungumi addinin kirista sau da kafa kana kuma ka da su yarda su bari son abin duniya ya yaudare su. A ranar lahadi shugaban na ´yan Katholika zai ziyarci tsohon sansanin gwale-gwale na Auschwitz dake kudancin Poland.