Panama ta kama wani jirgin ruwa na Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 16.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Panama ta kama wani jirgin ruwa na Koriya ta Arewa

Shugaban ƙasar Panama, Ricardo Martinelli ya ce sun kama jirgin ruwan ne saboda zaton da ake yi cewar yana ɗauke da makaman nukiliya.

Jirgin wanda ake kira da sunan Chong Chong Gan an kama shi a ranar Juma'a da ta gabata a gaɓar kogin Atlantika, daf da mashigin ruwa na ƙasar ta Panama kuma yanzu haka yana a tashar jiragen ruwa ta Manzanillo.

Shugaban ya ce da farko sun yin tsamani jirgin na ɗauke ne da miyagun ƙwayoyi to amma da aka fara sauke lodin da ke a kan jirgin, ya ce sai aka gano cewar yana ɗauke da shuga, sannan ya ce sun ga wasu na'urori waɗanda suke tsamanin na harhaɗa makaman nukiliya ne. Tun da fari dai matuƙin jirgin ya so ya kashe kansa gabannin binciken na 'yan sanda waɗanda sauran matuƙan suka so yin kafar ungulu gare shi. Shugaban dai na Panama ya ce za a gudanar da bincke mai zurfi domin gano abin da ke cikin jirgin wanda ya taso daga Kuba zuwa Koriya ta Arewa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh