1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Palmyra ya faɗa hanun dakarun gwamnatin Siriya

Abdourahamane HassaneMarch 27, 2016

Dakarun gwamnati Siriya waɗanda sojojin Rasha ke rufa wa baya sun sake ƙwace iko da garin Palmyra mai arzikin kayan tarihi da ke a yanki na tsakiya ƙasar.

https://p.dw.com/p/1IKX2
Syrien Palmyra Syrische Armee erobert Zitadelle
Hoto: picture-alliance/dpa/TASS/V. Sharifulin

Wani babban kwammandan dakarun ƙasar ya ce sun karɓe iko da garin baki ɗayansa kuma ya ce wannan nasara wani farko da kuma ƙarshe na Ƙungiyar masu jihadi ta IS ''Mun ragargaza Ƙungiyar 'yan tawayen ta IS a ciki da wajen Palymira kuma yanzu haka 'yan tawayen sun janye daga garin.''

A cikin watan Augusta na shekarar bara ne ƙungiyar ta IS ta ƙwace iko da garin na Palmyra, wanda hukumar raya al'adu da illimi ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta saka shi a cikin kayan tarihi na duniya.