1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Palesdinawa sun zargi Isra'ila da kai masu hari

August 15, 2014

Mahukuntan Falasdinu sun fara zargin Isra'ila da karya ka'idojin yarjejeniya tsagaita wutar da suka cimma ta kwanaki biyar.

https://p.dw.com/p/1CvZQ
Hoto: DW/Bettina Marx

Ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu da ke yankin Zirin Gaza ta zargi Isra'ila da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma ta hanyar yin barin wuta a garin Khan Younis da ke da kan iyaka wanda kuma ya ke karkashin ikon kungiyar Hamas. Sai dai a hannu guda kakakin gwamnatin Isra'ila ya musanta wannan zargi inda ya ce basu da masaniya akan wani batu mai kama da kai hari a yankin Falasdinawan. A ranar Alhamis din nan ne dai aka sabunta yarjejeniyar tsagaita wutar da za ta kwashe tsahon kwanakin biyar biyo bayan cikar wa'adin ta kwanaki ukun da suka cimma tun da farko. Tsagaita wutar na wannan karon dai shine mafi taho tun bayan da bangarorin biyu suka fara tattaunawa a kasar Masar domin kawo karshen zubar da jinin da aka kwashe tsahon kwanaki 29 ana yi a yankin Zirin gaza na Falasdinu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu