Palastinu ta zama ′yar kallo a Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 30.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Palastinu ta zama 'yar kallo a Majalisar Dinkin Duniya

Hakar palastinawa ta cimma ruwa bayan da ta samu amuncewar Majalisar Dinkin Duniya a zauren,a matsayin cikkakiyar kasa 'yar kallo.

default

Mahmud Abbas a Majalisar Dikin Duniya

Palastinu ta shiga sahun kasashe mambobin majalisar dinkin duniya a matsayin 'yar kallo,a yayin kada kuri'ar da a ka yi a daren jiya Alhamis. A kalla kasashe 138 ne suka kada kuri'ar amuncewa yayinda 9 suka kada kuri'ar kin amuncewa ciki har da Amurka da Isra'ila,sai kuma kasashe 41 da suka kada kuri'ar ba ruwan su daga cikin jimlar kasashen duniya 193 da ke wakilci a majalisar dinkin duniyar.
Jim kadan bayan kada kuri'ar dubban palastinawa ne suka fito kan tituna domin nuna farin cikinsu ga abun da suka kira gagarumar nasara a kan abunkan gaba.Kazalika kungiyar kishin islaman Hamas ta aikawa shugaban hukumar Palstinawa Mahmud Abbas sakon taya murna ga abun da ta kamata da tarihi mafi karfi ga gwagwarmayar da palastinawa ke yi.
Wannan matakin dai zai iya baiwa Palstinawan damar shiga kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifufuka da ke birnin Hage. Amurka da Isra'ila dai sun yi barazanar datse talafin kudaden shigar da suke baiwa palastinawan a nan gaba.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Usman Shehu Usman