1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun kolin Pakistan ta ce majalisa ta dawo

Abdullahi Tanko Bala
April 7, 2022

Firaministan Pakistan Imran Khan zai fuskanci matakin tsigewa bayan da kotun koli ta ce rusa majalisar dokoki da firaminista ya yi haramtacce ne kuma lallai ne majalisar ta ci gaba da kada kuri'ar rashin amanna.

https://p.dw.com/p/49dPC
Pkistan I Imran Khan
Hoto: Akhtar Soomro/File Photo/REUTERS

Kotun kolin Pakistan ta yanke hukuncin cewa matakin da Firaminista Imran Khan ya dauka na rusa majalisar dokoki haramtacce ne ta kuma bada umarnin majalisar ta cigaba da shirinta na kada kuri'ar rashin amanna.

Kotun dai ta yi umarni majalisar ta dawo a ranar 9 ga wannan watan na Afrilu domin cigaba da kuri'ar rashin amannar.

Yan adawa sun ce suna da kuri'u 172 da ake bukata daga cikin kujerun majalisar dokokin 340 domin tsige Firaministan.