Pakistan za ta ci-gaba da zartas da hukuncin kisa kan ′yan ta′adda | Labarai | DW | 17.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pakistan za ta ci-gaba da zartas da hukuncin kisa kan 'yan ta'adda

Gwamnati ta ce ba za ta tattauna da 'yan Kungiyar Taliban reshen Pakistan ba, kuma za ta ci-gaba da daukar matakan soji a kansu.

Bayan kisan gillan da kungiyar Taliban ta masu kaifin kishin addini ta yi a wata makaranta da ke Peshawar, gwamnatin Pakistan ta ce za ta ci-gaba da aiwatar da hukuncin kisa a kan 'yan ta'adda. Ofishin Firaminista Nawaz Sharif ne ya ba da wannan sanarwa, inda ya kara da cewa gwamnati ba za ta tattauna da 'yan Kungiyar Taliban reshen Pakistan ba, kuma za ta ci-gaba da daukar matakan soji a kansu. A ranar Talata mayakan Taliban a Pakistan wato TTP suka farma wata makaranta inda suka hallaka mutane fiye da 140 akasari yara kanana. Kasashen duniya gaba daya sun yi tir da wannan harin da ke zama irinsa mafi muni. Ita ma kungiyar Taliban a Afghanistan ta yi Allah wadai da harin da cewa ya saba wa koyarwar addinin Musulunci. Yanzu haka dai an fara zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar ta Pakistan.