Pakistan ta zargi Amirka da katsalandan | Labarai | DW | 03.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pakistan ta zargi Amirka da katsalandan

Bayan da Amirka ta kai harin da ya hallaka shugaban Taliban Hakimullah Mehsud ba tare da izininta ba, gwamnatin Pakistan ta ce Amirka na yi mata shisshigi a harkokinta na tsaro.

Gwamnatin Pakistan ta zargi takwararta ta Amirka da haifar da tafiyar hawainiya a yunkurin da take yi na sulhunta rikicin da ke tsakaninta da masu kaifin kishin addini na kungiyar Taliban. Wannan kuwa ya faru ne bayan da ita Amirka ta yi amfani da jirage maras matuka wajen kashe jagoran kungiyar Taliban Hakimullah Mehsud, kwana guda kafin kaddamar da taron zaman lafiya tsakanin sassan biyu.

Fadar mulki ta Islamabad ta gayyaci Jakadan Amirka a kasarta inda ta bayyana masa rashin jin dadin gwamnati game abin da ta danganta da shisshigin da Amirka ke yi mata a harkokinta na cikin gida. Ministan watsa labaran wannan kasa Pervez Rashid ya ce wannan kisan ba karamin dagula wa gwamnati lissafi ya yi ba a kokarin da take na cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban ba.

Tuni ma dai jami'an tsaron kasar ta Pakistan suka shiga cikin shirin ko ta kwana bayan kashe jagoran kungiyar Taliban Hakimullah Mehsud da kuma nada Sayed Khan a matsayin sabon jagora.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Saleh Umar Saleh