Pakistan na zaman makoki | Siyasa | DW | 17.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Pakistan na zaman makoki

Al' ummar Pakistan sun fara zaman makoki na kwanaki uku bayan mummunan harin da 'yan Taliban suka kai birnin Peshawar wanda ya hallaka kimanin mutane 141.

Galibin wadanda suka hallaka a harin dai kananan yara ne. Tuni dai wannan harin da aka kai a wata makaranta ta garin Peshawar ya fara shan suka a ciki da wajen kasar ta Pakistan. Daukacin 'yan siyasar kasar ta Pakistan sun yi amfani da zafafan kalamai wajen sukar abin da suka danganta da harin ta'addanci. Firaminista Nawaz Sharif wanda ya yi ta kokarin sasantawa da masu tsattsauran ra'ayin, ya fito karara ya canja matsayinsa game da wannan batu.

Canza shawara kan sulhu da 'yan ta'adda

"Muna kukan 'ya'yanmu da ba su ji ba, ba su gani ba da aka hallaka. Ko shakka babu za mu yaki 'yan ta'ada har sai mun ga bayansu. Za mu ci gaba da yaki, wannan babu tantama a kan wannan batu."

Makarantar da 'yan Taliban suka Kai hari a Peshawar

Makarantar da 'yan Taliban suka Kai hari a Peshawar

Suma dai 'yan Pakistan da ke da tsattsauran ra'ayin siyasa ba a barsu a baya ba wajen yin tofin Allah tsine ga abin da ya faru a Peshawar din. Sanannen dan wasan Kirket din nan Imran Khan wanda ke neman yin karan tsaye ga harkokin gwamnati tun shekarar da ta gabata ya bi sahu. A baya dai shi da magoya bayansa suna dora matsalar tsaro da Pakistan ke fama da ita a kan gwamnati da kuma kawayenta musamman ma Amirka. Amma kakakinsa Shireen Mirzi ta yi kira da a hada karfi da karfe domin kawo karshen ayyukan ta'addanci a kasar.

"Wannan hari ne da ya kamata a kwatanta da dabbanci. Lokaci ya yi da gaba dayan 'yan kasa za su hada kai domin yakar 'yan Taliban saboda sun ki amsa kiran da aka yi musu. Ba su da karfin tinkarar abokan gabarsu, shi ya sa suka juya kan kananan yara. To ba za mu yarda da wannan ba, dole ne mu juya wannan babi kwata-kwata."

Hada karfi waje guda domin yakar Taliban

Daya daga cikin 'yan Pakistan da suka tashi haikan wajen nuna adawa da manufofin 'yan Tliban ita ce Malala Yousafzai. Masu kaifin kishin addinin sun yi yunkurin kasheta a watan Oktoba na shekara ta 2012, amma kuma ba su yi nasara ba. Tun wannan lokaci ne matashiyar mai shekaru 17 da haihuwa a yanzu take fadi-tashi don ganin cewa kowanne yaro ya samu ilimi irin na zamani. Wannan ne ma ya sa aka bata lambar yabo ta Nobel a bana. A cewar ta nauyin kare yara daga hare-hare ya rataya ne a wuyan kowa da kowa.

Makarantu na addu'oi ga daliban da aka kashe a Peshawar

Makarantu na addu'oi ga daliban da aka kashe a Peshawar

"Ni da iyayena mun girgiza sosai bayan da muka samu labarin kashe yara da kuma malamai sama da 100. Yanzu lokaci ne da za a tashi tsaye. Ina kira ga kasashen duniya da kuma hukumomin Pakistan da ma jam'iyyun siyasa da mu hada karfi da karfe don yaki da ayyukan ta'adanci. Dole mu tabbatar da cewa kowane yaro ya samu kariya domin ya samu ilimi mai nagarta."

Tuni dai wannan kira na Malala ya fada cikin kunnuwan basira, domin kuwa sojojin gwamnati sun fara kai farmaki kan maboyar 'yan Taliban a kusa da kan iyaka da Afghanistan. Da ma dai 'yan Taliban sun kwashi kashinsu a hannu bayan da dakarun gwamnati suka shafe watanni suna kai musu jerin samame. Idan za a iya tunawa dai 'yan Taliban din sun yi ikirarin kai mummunan harin na Peshawar domin rama wa kura aniyarta. Saboda haka ne wani tsohon hapsan sojojin Pakistan din ya bayyana a shafinsa na Tweeter cewa: "Ba ni da tabbas an dora Pakistan kan tafarkin addini. Amma ina da tabbacin cewa addini zai iya zama sanadin wargajewar kasar."