1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: Mutum sama da 70 sun mutu a gobarar jirgin kasa

Binta Aliyu Zurmi
October 31, 2019

Wuta ta tashi a wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa lardin Punjab na kasar Pakistan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 70.

https://p.dw.com/p/3SHFY
Pakistan Zugunglück - Feuer in einem Passagierzug
Hoto: Reuters TV/A. Bhawalpuri

Lamarin ya faru ne yayin da guda daga cikin fasinjojin jirgin ke dafa abincin safe a lokacin da murhun gas din da ta ke amfani da shi ya fashe wanda nan take wuta ta kama.

A cewar ministan harkokin kula da sufurin kasar Sheikh Rashid Ahmed da yawa daga cikin talakawan kasar ta Pakistani na hawa jiragen kasa da murhunan girki duk kuwa da cewar doka ta haramta yin hakan. A kasar dai ba kasafai ake kula da bin ka'idojin cikin jirgin.