SiyasaJamus
Thailand: An zabi Paetongtarn, a matsayin firaminista
August 16, 2024Talla
Paetongtarn 'yar shekaru 37 wacce diyar Taxin Shinawatra,ce hamashakin attajirin nan kuma tsohon firaminista. Ta kasance ita kadai yar takara daya tilo a cikin kawancen masu rinjaye karkashin jam'iyyarta ta Pheu Thai a lokacin da aka kada kuri'ar zaben 'yan majalisar wakilai na nada shugaban gwamnati. Paetongtarn Ita ce firaministan Thailand ta uku daga zuria#r Shinawatra, bayan mahaifinta Thaksin wanda ya yi mulki daga shekara ta (2001 zuwa 2006) da kuma innarta Yingluck wadda ta yi mulki daga shekara ta (2011 zuwa 2014),wadanda dukkanisu aka yi musu juyin mulki.