Jamus: Ana binciken masu alaka da maharin Vienna
November 6, 2020Talla
Jami'an 'yan sandan Jamus sun kai samame gidaje da wuraren kasuwancin wasu mutane hudu, da ake zargin suna da alaka da maharin ta'addancin da ya halaka mutane a birnin Vienna.
Bayan gudanar da buincike kan mutanen a biranen Osnabruek da Kassel da kuma Pinnerberg, 'yan sandan sun ce ba a tuhumar mutanen kai tsaye da harin, amma akwai shedu da ke nuna mutanen na da wata alaka da wanda ya kai harin.
Mutane biyar ne suka mutu a harin ta'addanci ciki har da maharin, wasu mutane 20 sun jikkata har da dan sanda. Kasashen duniya sun yi tir da harin tare da neman daukar matakan hana aukuwar haka nan gaba.