Ostareliya za ta kwace fasgon ′yan jihadi | Labarai | DW | 26.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ostareliya za ta kwace fasgon 'yan jihadi

Firaminista Tony Abbot ya bayyana a ranar Talatan nan cewa duk wanda aka samu da zargin alaka da IS, za a hukunta shi tamkar wanda ke yaki da kasar ta Ostareliya.

Kasar Ostareliya ta shirya amincewa da wata doka cikin makonni da ke tafe, da za ta bawa gwamnati karfin iko na karbe takardun zama a kasa da wasu mutane ke da shedar zama a kasashe guda biyu, dokar da za ta yi aiki ne kan wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci koda kuwa ba a same su da laifi ba, kamar yadda Firaministan kasar Tony Abbot ya bayyana a ranar Talatan nan.

Fiye da mutane 100 ne 'yan kasar ta Ostareliya ake zargi da shiga kungiyar mayakan IS a Iraki da Siriya, inda kashi 50 cikin dari na wadan nan mutane ake ganin suna da takardun sheda ne ta zama a kasar ta Ostareliya da wata kasar.

A cewar Firaminsta Abbot kwaskwarimar da za a yi wa wannan dokar zama dan kasa, za ta sanya a hukunta masu goyon bayan kungiyar ta IS da ke ciki da wajen kasar ta Ostareliya, inda za a dauke su tamkar wadanda suka dauki makamai dan yakar kasar ta Ostareliya.