OPEC kungiya ta kasashen da ke da albarkatun man fetur a duniya. An girka ta ne domin duba yadda sha'anin da ya danganci hakowa da kasuwanci mai ke gudana.
A cikin shekarar 1960 ne aka kafa kungiyar ta OPEC wadda yanzu haka ke da ofishinta a birnin Vienna na kasar Ostiriya. Wasu daga cikin wakilan kungiyar sun hada da Saudiyya da Najeriya da Iran da Angola da Hadaddiyar Daular Larabawa.