1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Omoyele na son kawo canji a unguwar matalautan Legas

Mohammad Nasiru Awal
May 23, 2017

Isaac Success Omoyele ya tashi ne a unguwar Ajegunle da ke Legas. Sau tari yana barin makaranta. Sai dai rayuwarsa ta canja lokacin da ya samu tallafi na sukolaship. Yanzu yana taimaka wa marasa galihu a unguwarsu. Yana kuma taimaka wa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa da mata matasa a Legas don su kammala karatun boko.

https://p.dw.com/p/2dTEm