1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa tsakanin Scholz da Biden

Abdourahamane Hassane
March 3, 2023

An shirya shugabannin biyu za su tattauna batun kara ba da makamai ga Ukraine wadanda suka hada da tankokin yaki masu sulke.

https://p.dw.com/p/4ODjh
G7-Gipfel - Abschluss | Joe Biden und Olaf Scholz
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Gwamnatin Rasha ta yi gargadin cewar, yunkurin kara ba da makamai ga Ukraine ba zai warware yakin da ake yi ba, sai ma kara tsaiwaitashi. Fadar gwamnatin Rashar Kremlin, ta yi wannan furuci gabannin ganawar da ake shirin yi tsakanin shugaban Amirka Joe Biden da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da zai kai ziyara a Amirka. An shirya shugabannin biyu za su tattauna batun kara ba da makamai ga Ukraine wadanda suka hada da tankokin yaki masu sulke