Odinga zai ci gaba da bijirewa gwamnati | Labarai | DW | 31.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Odinga zai ci gaba da bijirewa gwamnati

Madugun 'yan adawar Kenya Raila Odinga ya bayyana cewa za su matsa lamba wajen ganin an girka wani tsari da al'umma za ta jagoranci kasar da kanta har sai an kai ga samun sahihiyar gwamnati.

Ya sanar da hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a wannan Talata inda ya ce za su ci gaba da shirya tarukan gangami da zanga-zanga domin bijirewa gwamnatin ta Shugaba Kenyatta. Sai dai kuma bai fito fili ya bayyana rashin amincewar shi da sakamakon sabon zaben da aka gudanar a kasar da Shugaba Kenyatta ya sake lashewa da sama da kashi 98 cikin dari.

Masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai sun bayyana cewa zaben bai kiyaye ka'idojin demokradiyya ba. A kan haka ne suka yi kira ga bangarorin biyu masu hamayya da juna hawa tebirin tattaunawa domin fahimtar junansu. Madugun 'yan adwar kasar ta Kenya Raila Odinga da magoya bayansa dai sun kaurace wa zaben na ranar 26 ga wannan wata suna masu bayyana shi a matsayin haramtacce. Ana sa ran dai nan ba da jimawa ba madugun 'yan adawar zai kalubalanci zaben a gaban kotun kolin kasar wacce ta soke zaben farko na watan Agusta a bisa dalillai na kura-kurai da ta ce an tafka a cikin zaben.