Obama zai taimaka wa Afirka yaki da Aids | Labarai | DW | 26.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama zai taimaka wa Afirka yaki da Aids

Amirka ta yi alkawarin tallafawa kasashen Afrika da miliyoyin daloli don magance yaduwar kwayar cutar HIV tsakanin yaran mata kanana.

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya sha alwashin tallafa wa kasashen Afrika da kudade har kimanin dala miliyan dari uku a karkashin wani shiri da zai kai ga magance matsalar cutar HIV ga yara mata kanana da suke fuskantar matsalar.

Ana so shirin ya zai kai ga cimma kashi 25 cikin dari na rage bazuwar cutar ga yara mata masu shekaru 15 zuwa 24 nan da karshen wannan shekarar da kuma samun raguwar kashi 40 cikin dari nan da shekara ta 2017.

Mai baiwa shugaban Amirkan shawara ta fuskar tsaro Susan Rice ta ce babu wani abu da ake bukata yanzu illa karfafa wa yaran gwiwa domin yakar cutar Hiv ko Sida.

Kasashen Afirka goma ne dai da suka hada da Kenya da Tanzaniya da Yuganda da Zambiya da Afrika ta kudu ragowar sun hada da Mozambik da Lesotho da Malawi da Zimbabwe ne zasu fara cin gajiyar tallafin daga Amirka.