Obama ya lashe zaɓen shugaban Amirka | Siyasa | DW | 07.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Obama ya lashe zaɓen shugaban Amirka

Barrack Obama na Demokrats ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa mai sarkakkiya, inda ya doke abokin takararsa na Republikan Mitt Romney.

Shugaban Amurka mai ci a yanzu kuma ɗan jam'iyyar Democrats, Barrack Obama ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa mai sarkakkiya, inda ya doke abokin takararsa na Republican Mitt Romney. Wannan zai bashi daman cigaba da mulkin Amurka na karin shekaru huɗu nan gaba.

Hausawa dai kance rana bata ƙarya, ranar shida ga watan Nuwamban da duniya ta sawa ido ta zo ta shige, kuma kamar yadda miliyoyin mutane suka yi hasashe, Barack Obama ne ya lashe wannan zaɓe, da aka kiyasta cewar shine mafi tsada a tarihin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar ta Amurka.

Obama ya doke abokin takarar tasa ne a wasu manyan jihohin Amurkan, duk kuwa da tarin matsalolin durkushewar tattalin arziki da rashin aikin yi da ƙasar ke fama dasu, masu kaɗa ƙuri'u a Amurkan sun gwammace cigaba da kasancewa da BaAmurke baƙin fata na farko daya shuganaci ƙasar, amaimakon abokin takararsa kuma attajiri, Mitt Romney.

USA Wahl Wahltag 2012 Mitt Romney Eingeständnis Wahlergebnis

Mitt Romney

Sakamakon zaɓen dai ya nunr da cewar Obama ya lashe zaɓen ne da da ɗan karamin rinjaye a jihohin Ohayo, Wisconsin, iowa/Aiwa, Pennsylvania da New-Hampshire, dake zama wuraren da Romney yayi takara. A yayin da shi kuma Romney ya lashe jihar North Carolina da gagarumin rinjaye.

Nasarar da Obama ya samu a jihar Ohayo/ Ohio dai, itace ta bashi damar samun wakilan zaɓe 270 da ko wane ɗan takara yake bukata, domin shiga fadar gwamnati ta white house. Kazalika Obama ya lashe jihohin Virginia da Colarado, wanda ya danne sakamakon da ake tababa akai.

A martaninsa, ɗan takarar jam'iyyar Republican Mitt Romney ya taya Obama murna da wannan nasara daya samu da 'yan jam'iyyarsa da mai dakinsa wadda ya yabawa goyon bayanta da kuma Amurkawa wanda yace basuyi zaɓin tumun dare ba. Ya yi fatan cewar obama zai bi kyawawan manufofi wajen jagorantar Amurka.

USA Wahl Wahltag 2012 Anhänger der Demokraten Obama siegt

Murna da sakamakon zaɓe

A yayin da magoya bayan Obama ke cigaba da bukukuwan murna a headquatarsa dake Chikago, magoya bayan Romney a Boston sun kasance cikin zulumi, bayan an sanar da sakamakon zaɓen, inda daya wa daga cikinsu suka fara janye daga dandalin taron, kamar yadda kafofin yaɗa labaru mai hoto na talabijin suka nunar.

An bayyana zaɓen shugaban ƙasar ta Amurka da kasancewa mai sarkakkiya, wadda ta kasance ba wai tsakanin 'yan takara biyu kaɗai ba, amma mutane biyu dake da munufofi da suka sha banban da juna wa ƙasarsu.

Barack Obama shine shugaba na 44 a fadar gwamnati ta White House.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal

Sauti da bidiyo akan labarin