Obama ya bukasa cinikayya da kasar China | Siyasa | DW | 11.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Obama ya bukasa cinikayya da kasar China

Shugaba Barack Obama na Amirka ya yi amfani da ziyarar da ya ke yi a yankin Asiya wajen bunkasa ma'amala tsakanin kasarsa da China a fannoni daban daban.

Daya daga cikin abubuwan da Shugaba Barack Obama ya mayar da hankali yayin ziyarar da yake yi shi ne kan bunkasa hulda kan kasuwanci da kasar China wadda take samun habakar tattalin arziki a shekarun da suka gabata, abin da ke bata damar tasiri a tsakanin kasashen. China na hubbasa na ganin an kawar da shingen kasuwanci tsakanin kasashen Asiya da na tekun Pacific. Cinikayya tsakanin kasashen 12 ta kai na 40 cikin 100 na tattalin arzikin duniya.

Masana na ganin cewa majalisun dokokin Amirka da 'yan adawa na jam'iyyar Republican suka mamaye za su saka matsin lamba wa Shugaba Obama domin kulla hulda ta kasuwanci tsakanin kasashen. Shugaba Barack Obama na Amirka ya nuna mahimmanci aiki tare da China yayin jawabin da ya gabatar lokacin taro kasashen Asiya da Pacific da China ke daukan nauyi:

APEC Gipfel Gruppenfoto 10.11.2014 Peking

Shugabannin Asiya da dama ne suka halarci taron kolin

"China da Amirka za su ayi iki tare, domin duniya baki daya. Wannan shi ne abin ku masu sauraro ke bukatar ji. Za mu ci gaba da bunkasa hulda ta kasuwanci da zuba jari tsakanin kasashenmu biyu."

Amirka na ci gaba da tattaunawa ta fannoni daban-daban bisa hanyoyi kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen na Asiya. Kasashe da dama na kudu da gabashin suna ganin kara samun ci gaba sakamakaon bunkasa China da kuma yadda Amirka ke ci gaba da kasancewa a yankin.

Wani abu da ke da mahimmanci shi ne na tinkarar kungiyoyi masu matsanancin ra'ayi kamar kungiyar IS mai neman kafa daular Islama a kasashen Iraki da Siriya. Kuma tuni wasu kasashen kudu da gabashi Asiya suka yi alkawarin taimakawa wajen dakile hanzarin kungiyar, tare da ba da hadin kai wajen yaki da ayyukan ta'addanci.

China wadda take da karfin tattalin arziki da karfin soji, ta shiga takun saka da wasu kasashe bisa rikicin kan iyaka da suka hada da Vietnam da kuma Philippines a kaban tekun kudancin China. Sai dai Shugaban Xi Jinping ya nunar da cewa bunkasa tattalin arziki da aiki tare shi ne abin da yafi muhimmanci:

APEC Gipfel Xi Jinping Rede 11.11.2014

Shugaban China ya taimakawa kasar samun bunkasar arziki

"China za ta bayar da kimanin dalar Amirka bilyan 40 kan asusu gina wannan hanya da taimakawa kasashen da za a gina hanyar wajen bunkasa kayyayaki, da masana'antu, da kuma hadin kai a fannin kudade da sauran tsare-tsare."

Yanzu wani abin mai muhimmanci ga Shugaba Barack Obama na Amirka shi ne irin hulda da zai kulla da kasashe kudu da gabashin Asiya yayin da ya halarci taron da za su gudanar a kasar Myammar ko Burma.

Sauti da bidiyo akan labarin