1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Novak Djokovic ya koma kasarsa

January 17, 2022

Zakaran kwallon Tennis din nan na duniya, Novak Djokovic, ya isa kasarsa ta haihuwa wato Serbia bayan hana shi izinin zama da Australia ta yi saboda rashin rigakafin corona.

https://p.dw.com/p/45dgF
Australien Abfahrt Gerichtssitzung Fall Djokovic
Hoto: James Ross/AAP/picture alliance

Matakin hukumomin kasar Australia na hana Novak Djonkovic izinin zama saboda rashin rigakafin, ya dakatar zakaran na Tennis daga fafatawa a gasar Australia Open da aka fara a wannan Litinin.

Tuni dai jirgin da ya dauko Djokovic wanda ya zango a Hadaddiyar Daular Larabawa ya sauka Belgrade babban birnin kasar Serbia.

Shi dai Mr. Djokovic dai ya yi kokarin kotun Australia ta ba shi damar zama a kasar saboda gasar ta Australia Open, ganin cewa bisa ka'ida ba lallai ba ne sai ya nuna shaidar rigakafin coronar ba.

Gwani na gwanayen kwallon na Tennis, ya dai kamu da cutar a baya kuma ya warke abin da kimiyya ta ce ba ya bukatar rigakafin.