Norway ta tsare wasu matukan jirgin Latviya | Labarai | DW | 08.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Norway ta tsare wasu matukan jirgin Latviya

An samu matukan jirgin na kamfanin jiragen sama na Lettone Air Baltic sun yi tatul barasar da ta wuce kima a lokacin da suke shirin daukar fasinja.

Hukumomin kasar Norway sun kama wani direban jirgin sama na kamfanin jiragen saman Lettone Air Baltic na kasar Latviya da wasu abokan aikinsa su uku, bayan da suka same su sun yi tilip da barasa a daidai loakcin da suke shirin tashi daga birnin Oslo zuwa birnin Chania na kasar Girka da fasinjoji 109. Wani mutun ne ya kira 'yan sanda ta waya da misalin karfe biyu agogon GMT, inda ya sanar da su halin mayen da ya iske direban jirgin da sauran abokan aikin na sa a daidai lokacin da suke haramar hawan jirgin.

Binciken da hukumomi kasar ta Norway suka gudanar a kan matukin jirgin da abokan aikin nasa ya nunar da cewa akwai adadin sinadarin alkol din barasa da ya wuce kima a cikin jinin kowanensu. Tuni dai a cewar shugabar hukumar 'yan sandar garin Romerik na kasar a Norway suka tsare matukan jirgin tare ma da iza keyarsu zuwa gidan asibiti domin zurfafa binciken gano adadin giyar da suka kwankwada.

Idan har binciken ya tabbatar da sun kwankwadin giyar da ta zarce kima to kuwa ko wanensu na iya fuskantar hukuncin zaman kaso na tsawon shekaru biyu.