1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nkurunziza ya yi rantsuwar kama aiki

Nura Datti Kankarofi/PAWAugust 20, 2015

An wayi garin alhamis da rantsar da shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza a wa'adinsa na uku, abin da ya baiwa al'umma mamaki.

https://p.dw.com/p/1GJ4u
Burundi Pierre Nkurunziza
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Karaba

An dai rantsar da Shugaba Pierre Nkurunziza karo na uku wanda kuma da dama daga cikin mutane ke ganin ya sabawa doka, sakamakon yadda shugaban yayi kaka gida ya dare gadon mulkin a karo na ukku cikin murdiya da kuma wani abu mai kama da tilastawa jama`ar kasar da ma sauran al`ummar duniya, sai dai yayin rantsuwar kama aikin Shugaban yayi alkawarin dawo da doka da oda a kasar tare kuma da kokarin ganin ya samar da wani yanayi da zai janyo hankalin yan kasar na su bayar da goyan baya don samar da dawwamammen zaman lafiya, hadin kai da kuma cigaban kasa.

A ranar 26 ga watan Augustan da muke ciki ne aka ayyana rantsar da Shugaban, amma kuma kwatsam sai aka rantsar da shi ba zato ba tsammani a Alhamis din, al´amarin da Innocent Muhozi shugaban tawagar yan jaridun kasar da suka saka idanu yayin zaben ke ganin sake tunanin da Shugaban yayi, yana da alaka da yanayin da kasar ke ciki wanda kuma komai zai iya faruwa.

A tunani na shugaban ya canja shawara ne saboda rashin tsaro da zaman lafiya wanda kuma muddin ana cikin irin wannan yanayi to kuwa komai ka iya faruwa, kasan cewa babban abin da kasa ke bukata shine tsaro, idan kuma babu shi to ba zaman lafiya.

Akwai abubuwa da dama da ke janyo fargaba

Wani babban al`amari da har yanzu ke dada tsoratar da al`ummar kasar shine koma bayan tattalin arziki, wanda kuma yan kasar ke kokawa a dai dai lokacin da ake cigaba da jin karar harbe harbe cikin dare, lamarin da kuma suke zargin cewa an ya kuwa da gaske ne kasar na fama da rashin kudi, batun da Jumane Athumani wani mazaunin birnin Bujumbura ke musun cewa da kudi ne fa ake sayan alburusai da kuma makamai.

Burundi Vereidigung Präsident Nkurunziza
Hoto: Reuters/E. Ngendakumana

Zan kasance na nuna son kai idan har na ce babu komai, tun da a cikin unguwanni ana ta jin karar fashewar abubuwa, abun da ke nuni da cewa kenan akwai makamai, idan kuma ana kwashe tsawon dare ana amfani da irin wadannan makamai ai ka ga da kudi ne ake sayansu, don haka abu ne mai daure kai sosai, kuma mai muni.

Hasashen makomar Burundi

Abun da dai yanzu jama`a ke hankoran gani shi ne yadda kasar za ta kasance a karkashin mulkin shugaban da ake ganin na samun zazzabar adawa daga yan adawar kasar da kuma suka ki shiga a dama dasu a zaben, sai dai a ganin Yoland Buka da ke aiki a cibiyar nazarin tsaro dake a Nairobin Kasar Kenya akwai bukatar agajin kungiyoyin kasashen Afrika don kawo karshen lamarin.

Babban abu mafi mahimmanci shi ne Kungiyar kasashen gabashin Afrika su bujuro da wani yanayi da zai kawo karshen balahirar, ta kiran bangaren Shugaban kasar da kuma na yan adawa tare da jin korafin kowanne bangare da kuma samar da matsaya daya tilo da zata kasance tubalin zaman lafiya mai dorewa.

Kasashe da dama gaske dai basu halacci rantsar da Shugaban ba, illa kasar Afrika ta kudu da ta aika da wakilcin minista, sai kuma Tanzaniya da Rasha da dai sauransu.