1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nkurunziza ya fara ikirarin yin nasara

Yusuf Bala/PAWJune 30, 2015

Shugaban Burundin na ikirarin lashe zaben 'yan majalisan ne duk da cewa kungiyoyin kare hakkin bil'adama na cikin gida da waje sun kauracewa zaben.

https://p.dw.com/p/1FqC7
Parlamentswahlen in Burundi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Ngingo

An dai yi zaben 'yan majalisar na ranar Litinin ne babu armashi, kasancewar jam'iyyun adawa sun kaurace masa sannan babu yawaitar masu kada kuri'a, wasu na buya a gida saboda fargabar tashin hankali, wasu kuwa dubbai tuni sun tsallake daga kasar suna neman mafaka a kasashe da ke makwabtaka da Burundi irisu Tanzaniya da Jamhuriyar Demokardiyar Kwango.

Ganin yadda sama da mutane 70 suka rasa rayukansu tun bayan da kasar ta fada rikicin siyasa, da bangaren adawa ke cewa neman tazarcen shugaba Nkrunziza karo na uku ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Ra'ayoyin wadanda suka kada kuri'a

Ga wadanda suka yi ta maza suka kada kuri'arsu irinsu Niyangabo Bienvenu sun tsaya ne su yi zabe dan kare hakkinsu karkashin demokradiya:

A matsayina na dan kasa mai 'yanci hakkina ne na yi zabe ta yadda zan zabi shugaban da na ke so ya jagorance ni ta haka ne za ka sami sauyi irin wanda ka ke so.

Shi kuwa Jean Claude cewa ya yi wannan rana ita ce da al'ummar kasar suka dade suna jira ta zo.

Parlamentswahlen in Burundi
Wasu sun zauna a gida domin fargabaHoto: AFP/Getty Images/L. Nshimiye

Ina cikin matukar farin ciki domin wannan rana ce da muka dau kilokaci mai tsawo muna jiran ta zo , muna kaunar kasarmu, kuma idan mutum na kaunar kasar sa sai ya karetata hanyar zaben shugabanni da ke da kyakkyawan fata za su kare maka kasarka.

Tuni dai kasashe na duniya da suka hadar da Amirka suka bayyana rashin gamsuwa da wannan mataki na mahukuntan kasar ta Burundi inda suka yi gaban kansu suka gudanar da zabe duk kuwa da kiraye-kirayen kasa da kasa na cewa yanayin da kasar ke ciki bai kamata a yi zabe ba ganin koda a ranar zaben wasu makaman gurneti sun tashi a wasu mazabu ban da wadanda suka tashi a jajiberin zaben ba a maganar watanni na zanga-zangar adawa da shirin tazarce da ta lakume rayukan jama'a.

Parlamentswahl in Burundi
Kasashen duniya na adawa da zabenHoto: picture-alliance/dpa/D. Kurokawa

Kasar ta yi gaban kanta wajen yin zabe

To ko me ya sa mahukuntan wannan kasa suka dauki wannan mataki Willy Nyamitwe shi ke magana da yawun shugaban kasar ta Burundi.

Suna tunanin cewa babu tsaro, suna ganin yanayi da kasar Burundi ta shiga ba zai yi wuwu a yi zabe mai inganci ba amma a karshe mun tabbatar musu da cewa za mu iya gudanar da zabe ba tare da wata matsala ba.

Masu sharhin dai kan lamuran zabe sun bayyana cewa sharuda da ake bukata zabe ya inganta mafi kankanta sun hadar da barin 'yan jarida su gudanar da ayyukansu ba tare da shamaki ba sannan duk masu dauke da makamai musamman matasan Imbonerakure da 'yan uwansu da ke mara baya ga shugaban kasa su ajiye makamansu. Kafin ma a zo ga bartun sanya idanun kasa da kasa.