Nijeriya:Cheif Ernest Shonekan ya rasu | Labarai | DW | 11.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijeriya:Cheif Ernest Shonekan ya rasu

Rahotanni daga birnin Legas da ke kudancin Najeriya na cewar tsohon shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Cif Ernest Shonekan ya rasu.

Masu aiko da rahotanni suka ce Shonekan, mai shekaru 85 ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin na Legas sai dai ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance abin da ya yi ajalinsa ba.

Cheif Shonekan ya jagoranci gwamnatin rikon kwaryar Najeriya tsakanin ranar 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban shekarar 1993, bayan da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya sauka daga mulki.